Darma za ta kara yin illa ga rayuka a Zamfara

hakar zinari a Najeriya
Image caption Darma tana illa a boye

Kungiyar kare muhalli ta Blacksmith Institute ta yi gargadin cewa daruruwan yara za su iya mutuwa a sanadiyyar illa daga gubar dalma a jihar Zamfara ta Nijeria, inda jama'a ke tono zinari ko kan ka'ida ba.

Wannan gargadi dai ya zo ne kwana daya bayan da jami'an gwamnati Nijeriar suka tabbatar cewa mutane 163, galibinsu yara, sun rasa rayukansu a sanadiyyar illar da suka samu daga gubar dalma, tun daga watan Maris na bana.

Wakilin BBC ya ce ma'aikatan asibiti da gwamnatin Nijeria suna jinyar wadanda abun ya shafa, kuma tuni aka kwashe jama'a daga wasu sassa na kauyukan da al'ammarin ya shafa.

Kungiyar ta Blacksmith Institute dai ta ce wani gwaji da ta yi ya nuna cewa matasa da dama a arewacin Nijeria suna da gubar dalma mai yawa a cikin jininsu.