Za a shiga gyaran muhalli a Naija Delta

Taswirar Najeriya
Image caption Ko a wannan karon za a ga sauyi?

A wannan rana ta yau, ta kula da muhalli a duniya, jihar Ribas dake kudu maso kudancin Najeriya ta kuduri aniyar dawo da martabba kasar noma, da rafuka da kuma dazuzzuka da ke yankin.

Makasudin ware ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi don maida hankali ga kare muhalli, shi ne illar da rashin kare muhalli ke kawowa.

Wata kididdiga ta majalisar dinkin duniya ta ce halittu( tsakanin tsirai da tsuntsaya,da sauran namun daji) kimanin miliyan 15 ke kokarin bacewa daga doron kasa a duniya sanadiyar tabarbarewar muhalli

Yankin Niger-Delta yana daya daga cikin yankunan duniya da suka gamu da gurbatar muhalli, inda man da ake hakowa a yankin ya bata ruwaye, da kasar noma, da kifaye da lafiyar jama'a.