BP na da karfin gwiwar katse malalar mai

Tsuntsu, malalar mai ya kassara
Image caption Ko karshen wahala ta kusa ke nan?

Shugaban kamfanin mai na BP ya nuna kwarin gwiwa game da kokarin da kamfaninsa ke yi na dakatar da man da ke malala a tekun Mexico da kuma gyara barnar da al'ammarin ya yiwa muhalli.

A wata hira da BBC, Tony Hayward ya ce na'urar da aka dasa jikin bututun da ya fashe, tana tare ganga dubu goma na man a rana, kuma wasu karin na'urorin da za a kafa nan da karshe mako mai zuwa, za su taimaka wajen tare galibin man da ke tsiyaya.

Hakazalika Mr Hawyard ya yi alkawarin cewa kamfanin na BP zai kwashe man da ya malala.

Ya ce, “Za mu dakatar da tsiyayar man; za mu kwashe man, mu kuma gyarar barnar da ya haddasa ta yadda tekun na Mexico zai koma kamar yadda yake kafin aukuwar wannan hadarin.”