Hukunci game da hadarin Bhopal na India

Masana'antar da hadarin ya faru a Bhopal
Image caption Masana'antar da hadarin ya faru a Bhopal

Wata kotu a India dake zamanta a garin Bhopal, ta yankewa mutane takwas hukunci, game da yoyon iskar gas mai-guba da ya faru shekaru 25 da suka wuce, wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.

An sami mutanen guda takwas da laifin sakaci da kuma sandiyyar mutuwar jama'a.

Wannan dai shine karo na farko, a hukunce da aka kama wasu da laifi kan hadari a masana'antu da ake ganin, shine mafi muni da aka samu a duniya.

Haka kuma hukuncin ya zo ne bayan mutuwar daya daga cikin wadanda aka samu da laifin. Sauran mutanen bakwai dai, an yanke mu su hukuncin shekara biyu a gidan kaso da kuma tara.