Majilisar dinkin duniya zata jefa kuria kan Iran

Iran
Image caption Wani dakin gwajin nukliya a Iran

Kwamitin Sulhu na Majilisar dinkin duniya zai jefa kuriar kafawa Iran sabon takunkumi

A gobe laraba ne ake saran cewa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, zai kada kuri'a na amincewa da kudirin daya cimma na sanya wani sabon takunkumi, kan kasar Iran.

Takunkumin dai ya karkata ne kan shirin nukiliyar kasar ta Iran, wanda kuma idan aka amince dashi zai tsaurara hada hadar kasuwanci da binciken jiragen ruwan Iran dake dauke da kayayyaki, tare kuma da fadada haramcin mallakar makamai

Sai dai lokacin da za'a jefa kuriar, ya danganta ne akan matsayar da wakilan diplomasiyar zasu cimma, kan jerin sunnayen yan ta kasar da wanan takunkumin zai shafa, da kuma kadororin da za'a kwace da kuma hana su yin tafiye tafiye

Ammah kuma akwai wasu kasashen da zasu ki jefa kuriarsu kokuma zasu kada kuriar nuna rashin amincewa .

Wakiliyar tace kasashen sun sun hada da Turkiya da kuma Brazil, wadanda suka ce sabon takunkumi kan Iran ba zai yi tasiri ba .

Sun ce yarjejeniyar da suka cimma da kasar ta iran akan makamshin nukiliya, wata dama ce ta samun daidaito a fuskar diplomaciya .