Sojin israila sun kashe Falasdinawa biyar

Sojin ruwan`kasar Israila sunce sun kashe wasu Palasdinawa biyar wadanda ke dauke da muggan makamai akan hanyar su ta kaiwa Israilar hari .

Rundunar sojin kasar ta ce mutanen data kashe dai, na amfani ne da wani`karamin jirgin ruwa, a wani wuri dake kusa da yankin Gaza, lokacin da sojojin ruwan suka hango su, inda daga bisani suka bude musu wuta.

Kungiyar Fatah na Palasdinawa dai, ta ce an kashe hudu daga cikin mayakanta inda kuma mutum na biyar har yanzu ba'a san inda ya ke ba.

Harin na zuwa ne a dai dai lokacin, da shugaban Falasdinu Mahamoud Abbas Ke kasar Turkiya, domin halatar wani taron da ya shafi tsaro a yankin Gabas ta tsakiya.

Ana kuma sa ran cewar zai tattauna da shugaban kasar Turkiyar kan rawar da kasar zata taka a yankin Gabas ta Tsakiya