An kashe mutane a rikicin achaba na Jos

wasu jami'an 'yan sandan Nijeriya
Image caption 'Yan sandan Nijeriya, dai na shan suka wajen take hakin bi'adama.

Rahotanni daga Jos, babban birnin jihar Plateau a Nijeriya na cewa mutane akalla shidda ne suka rasa rayukansu , a wata arangama tsakanin 'yan sanda da masu sana'ar hanyar babura, da aka fi sani da suna 'yan Achaba.

'Yan sandan sun fara cafke 'yan Achabar ne, a yunkurin fara aiki da wata doka wadda jihar ta kafa, wadda ta haramta sana'ar Achaba a cikin birnin Jos da kewaye.

Birnin Jos dai yayi ta fama da tashin hankali mai nasaba da addinin da kuma kabilanci.

Su dai hukumomin jihar ta Pilato na zargin 'yan achabar da aikata miyagun laifukka, da kuma kasancewa a gaba gaba a duk lokacin da ake wani tashin hankali.

'Yan Achabar dai na zargin cewa gwamnatin jihar Pilaton ta dauki matakin hana sana'ar ce domin Hausawa ne ke yi.