An yi artabu tsakanin 'yan sanda da 'yan Achaba a Jos

Taswirar Nijeria
Image caption Taswirar Nijeria

Rahotanni daga Jos baban birnin jihar Plateau dake Tsakiyar Nijeria na cewa yanzu haka kura ta lafa a birnin na Jos, bayan wani tashin hankali tsakanin 'yan sanda da wasu masu sana'ar Achaba.

'Yan Achaban sun yi ta jifa da duwatsu , tare da cinna tayoyi wuta a kewayen tsakiyar birnin, bayan da 'yan sanda suka yi kokarin hana su gudanar da sana'arsu.

A kwanakin baya ne dai hukukomin jihar suka kafa dokar haramta sana'ar ta Achaba a cikin garin Jos da kewaye.

Hukumomin jihar dai na zargin su ne da hannu a rikicin addini da na kabilanci da aka yi a jihar, lamarin da masu sana'ar suka yi ta korafi a kansa.