Za a fara share gubar dalma a zamfara

mahakar zinariya a jihar Zamfara ta Nijeriya.
Image caption kasar wasu kauyukan jihar Zamfara ta gurbace da gubar dalma.

Ma'aikatar Lafiyar Najeriya ta bayyana cewa an shawo kan annobar gubar sinadarin dalma da ta barke a jihar Zamfara, da ke arewacin kasar.

Ma'aikatar dai ta bayyana cewa ana ci gaba da daukar matakan hana barkewar annobar a gaba, don haka jama'ar yankin su kwantar da hankalinsu.

Sama da mutane dari uku , wadanda mafi yawansu kananan yara ne suka harbu da cutar, a kauyuka biyar a kananan hukumomin Bukkuyum da Anka, yayin da sama da dari daya da sittin daga ciki suka mutu.

A gobe ake Talata ake sa ran fara aikin kwashe gurbatacciyar kasar dake shimfide a kauyukan, tare da maye gurbinta da wata sabuwa.