Akwai alamar tambaya a zaben badi- inji wasu yan Najeriya

Nigeria
Image caption Majilisar dokokin taraya Najeriya

A Najeriya gyaran fuskar da majalisun dokokin kasar,ke yi ga dokokin zaben kasar ya tabbata, inda a watan Janairun badi ne ake sa ran za a gudanar da babban zaben kasar. Sai dai kawo yanzu hukumar zaben kasar ba ta kammala yin wasu abubuwa da ake ganin ginshikai ne ga zaben ba, cikinsu har da sabunta rajistar masu kada kuri`a da rajistar jam`iyyun siyasa.

Rahotanni dai na nuna cewa kusan jam'iyyun siyasa sittin ne suka yi rajistar shiga zaben na badi, kuma wannan ne ya sa, wasu masu sharhi kan harkokin siyasa a kasar ke ganin cewa abu ne mawuyaci, hukumar zaben ta iya shirya zabe mai nagarta cikin dan lokacin da ya rage mata.

Babbar matsalar a cewar su itace,babu lokaci inda anyi la'akari da cewa watani shidda suka rage, a gudunar da zaben badi kuma ita, kanta hukumar ta INEC bata da kwamishinoni da kuma shugaban da zai jagoranci ayyukan hukumar.

Sai dai hukumar ta INEC ta bada tabaccin cewa zata sauke aikin dake gabanta.

Ta kuma ce a karshen watan da muke ciki, za'a fara sabunta rajistar masu kada kuri'a kuma yiwa jam'iyyu rajistar ba za zai kawo illa ga zaben kasar ba.