A yau Zamfara zata fara aikin kwashe kasa

Najeriya
Image caption Jihar Zamfara na yankin Arewacin Najeriya

A yau litinin ne hukumomin Jihar Zamfara dake Arewacin Najeriyar suka ce za su fara aikin debe kasar wasu kauyuka biyar dake Jihar

Hakan ya biyo bayan binciken da ya nuna cewar, kasar wadannan kauyuka sun gurbace da sinadarin Lead mai guba da ake kyautata zaton shi ya haddasa mutuwar sama da mutane dari da sittin, tare da jikkata wasu da dama.

Rahotanni sun bayyana cewa hakan ya faru sakamakon hako ma'adinai da wasu mazauna `kauyukan suka yi ba bisa kaida, tare da kawo duwatsun da suka hako, wadanda ke kunshe da sinadarin, zuwa cikin gari inda suke nike su domin neman zinari.

Wata jamiar kungiyar likitoci mai samar da agaji dake jinyar yaran da suka shakki iskar da dauke da gubar , Lauren Kooney ta fadawa BBC cewa wasu daga cikin yaran suna da sinadarin dalma mai matukar yawa a cikin jinisu .

Sai dai kuma ma'aikatar kiwon lafiyar a kasar ta ce ta kafa wani kwamiti na masu ruwa da tsaki, wanda zai rika taro akai akai domin shawo kan matsalar da kuma hana aukuwar ta a gaba.