An fara kwashe kasa mai gubar dalma a Zamfara

Masu hakar kasa don neman gwal a Zamfara
Image caption Kasar da mutanen kauyukan ke hakowa dai na dauke da sinadarin dalma mai guba.

Ana cigaba da kwashe kasar data gurbata da sinadarin dalma a garin Dareta dake karamar hukumar Anka a jihar Zamfara.

Hukumomi sun dauki wannan matakin ne domin kawar da hadarin da ke barazana ga lafiyar jama'ar garin, biyo bayan samun sinadarin dalmar a jikinsu.

Matsalar dai ta shafi kauyuka shida ne a jihar, kuma kawo yanzu dai kimanin mutane dari da sittin ne suka mutu, kuma mafi yawa daga cikinsu kananan yara ne.

An kafa sansanonin cibiyoyin kula da lafiya na gaggagawa, inda ake kai yara 'yan kasa da shekaru biyar wadanda sukafi kamuwa da shakar gubar dalmar.