An bukaci kakakin majalisar wakilan Najeriya yayi murabus

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Gungun wasu 'yan majalisar wakilan Najeriya sun yi kira ga kakakin majalisar da ya sauka daga kan mukaminsa nan da kwanaki bakwai, idan kwa ba haka ba za su yi kokarin tsige shi.

A cewar 'yan majalisar wakilan, kakakin majalisar, Dimeji Bankole, yana yin mulkin kama karya da kuma keta dokokin tafiyar da majalisar.

Sai dai masu goyon bayan kakakin majalisar sun ce, wadannan zarge-zarge ba su da tushe, suna masu cewa, wasu ne kawai ke kokarin kawo baraka a majalisar.

Tun bayan tube wasu daga shugabancin wasu kwamitoci ne dai ake ta samun kace-nace a majalisar wakilan ta Najeriya.