An kakkabo jirgin Nato a Afghanistan

Hari kan sojojin Nato a Afghanistan
Image caption Sojojin Nato na fuskantar hare-hare daga masu tayar da kayar baya

Akalla sojojin kungiyar tsaro ta Nato hudu ne aka kashe bayan da aka harbo jirgi mai saukar ungulun da suke tafiya a ciki, a yankin Helmand na kudancin Afghanistan. Wasu masu tada kayar baya ne "suka harbo jirgin", a cewar kungiyar ta Nato.

Jirgin ya fado ne a gundumar Sangin, kamar yadda mai magana da yawun gwamnan yankin Dawood Ahmadi, ya bayyana.

A wata gajeriyar sanarwa, kungiyar Taliban tace mayakan ta ne suka harbo jirgin da gurneti.

Mai magana da yawun kungiyar Yousuf Ahmadi, ya gayawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, jirgin ya fado a gundumar Sangin a ranar Laraba.

Kawo yanzu dai kungiyar tsaro ta Nato bata bayyana sunayen jami'an da abin ya ritsa da su ba ko kuma kasashen da suka fito.

Sai dai wakilin BBC Martin Patience yace jirage na cikin hadari a lokutan da suka zo sauka ko tashi, saboda barazanar hare-hare da suke fuskanta na rokoki da kuma bindiga.