An yiwa 'yan jarida fashi a Afrika ta Kudu

'yan sandan Afrika ta Kudu
Image caption 'yan sandan Afrika ta Kudu na da babban kalubale a gaban su

'yan sanda a Afrika ta Kudu sun ce an yiwa 'yan jaridar kasashen waje uku da ke daukar rahoto kan gasar cin kofin duniya fashi. Daya daga cikin su ya ga 'yan fashin a lokacin da suka kutsa masaukin su da sanyin safiyar Laraba.

"Daya daga cikin 'yan fashin ya nunawa 'yan jaridar bindiga sannan ya umarce shi da ya kwanta a kasa," a cewar mai magana da yawun 'yan sanda Hangwani Mulaudzi.

'yan jaridar wadanda biyu daga cikin su suka fito daga Portugal sannan daya daga Spaniya, basu samu rauni ba, sai dai an yi awangaba da kayansu da takardun shaidar su.

Kanal Mulaudzi yace 'yan sanda na fatan yin kamu nan gaba kadan, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na PA ya rawaito.

"Ni kadai ne na farka lokacin da 'yan fashin suka shigo dakin mu," daya daga cikin 'yan jaridar Antonio Fimoes, ya gayawa kamfanin dillancin labarai na AFP.

"Dayan su ya sanya mun bindiga aka, yayinda daya ya ci gaba da dibar kayanmu,".

'yan sanda suka ce wajibi ne masu hotel din da 'yan jaridar ke zaune su tsaurara matakan tsaro.

Kimanin mutane 350,000 ne ake saran za su ziyarci kasar saboda gasar cin kofin duniya, wacce za a fara a ranar Juma'a.

Kasar Afrika ta Kudu ta horas da dubban 'yan sanda domin samar da tsaro ga masu sha'awar kwallon da za su halarci gasar.