Burtaniya za ta kara tallafawa Afghanistan

Firayim Minista David Cameron da Shugaba Karzai na Afghanistan
Image caption Firayim Ministan Ingila David Cameron da Shugaba Karzai na Afghanistan

Firayim ministan Burtaniya, David Cameroon ya bada sanarwar karin fam miliyan sittin da bakwai da za a kashe wajen tunkarar barazanar bama-baman da ake danawa a gefen hanya aAfghanistan, a ziyararsa ta farko zuwa can, a matsayin Firayim minista.

A wani taron manema labaru da shugaban Afghanistan Hamid Karzai, Mr Cameroon ya jaddada cewa Afghanistan ce sahu gaba, cikin abubuwan da zai baiwa fifiko.

Kamar dai yanda Firayim Ministan ya bayyana, karin kudaden zasu taimakawa wadanda ke aikin kawar da bama baman a Afghanistan.

Wadansu nau'in makamai da aka fi sani da suna IEDs sune babbar barazanar da dakarun Burtaniya ke fuskanta, inda sukan yi ajalin daruruwa da ma raunata wadansu.

Ta'addanci

Sojin Burtaniya dai na fuskantar karin matsin lamba na fito da hanyoyin magance ta'addanci.

Ko a watan daya gabata sai da wani babban jami'in soji Kanal Bob Sedden yayi murabus dangane da fargabar cewa za'a sadaukar da horo.

Da yake yiwa manema labarai bayani a fadar gwamnatin Afghanistan din, David Cameron ya jaddada cewa wannan shekarar nada mahimmanci wajen ci gaba da samun daidaito a kasar.

Bayan kawar da batun aikewa da karin dakarun Birtaniya, ya dai bayyana cewa za'a kara yawan kudade ga jami'an Afghanistan din domin karawa dakarunta kwarin gwiwa:

"Batun tura karin dakaru dai baya cikin jerin abinda Birtaniya zata yi. Muna da dakaru da dama ba wai kawai na Burtaniya ba, har dana Amurka". Inji David Cameron

Firayim Ministan ya ce a lardin Helmand, akwai fiye da dakarun Amurka dubu ashirin dana Burtaniya kimanin dubu goma.

Ya ce yana ganin akwai mahimmanci barinsu domin cigaba da aikin da suke yi na samar da tsaro a lardin na Helamand.

Kwarin gwiwa

Mai masaukin nasa wato shugaba Hamid Karzai dai ya bayyana cewa yana da tabbacin cewa za'a yi nasara akan kungiyar Taliban. Ya dai kara ne da yiwa Birtaniya godiya:

"A madadin al'ummar Afghanistan, ina so na sake godewa Prime Ministan dangane da taimakon da al'ummar Birtaniya suka yi wa jama'ar Afghanistan, da kuma sha'awar da suka nuna a Afghanistan dama yankin". Inji Hamid Karzai

Wannan ne dai karo na farko da Mista. Cameron din ya kai ziyara Afghanistan tun bayan karbar mulki a watan daya gabata.

Kuma wannan ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da kusan sojojin kasashen yammaci ashirin suka rasu a yayin wani fada da kungiyar Taliban.