EFCC ta kama dan takarar gwamnan Kano

Taswirar Najeriya
Image caption An dade ana zargin jami'ai da cin hanci da rashawa a Najeriya

Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya, EFCC ta kama tsohon kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kano da wasu shugabannin kananan hukumomi uku.

Ana dai zargin Malam Salihu Sagiru Takai, wanda na daya daga cikin masu neman kujerar gwamna a jam'iyyar ANPP mai mulkin jihar.

Tare da shugabannin kananan hukumomin Nassarawa da Tarauni da Kabo da laifin batar da kudaden kananan hukumomin ba bisa ka'ida ba. Sai dai kakakin gwamnatin Kano ya ce wannan sharri ne na abokan adawar siyasa kasancewar tsohon kwamishinan shi ne mutumin da gwamnan Kano ya zaba ya gaje shi a zaben 2011.

Kakakin hukumar ta EFCC Mista Femi Babafemi ya tabbatar wa da BBC kamun da suka yiwa tsohon kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kanon, Malam Salihu Sagiru Takai.

Har ila yau yace baya ga kwamishinan, akwai shugabannin kananan hukumomi da aka kama shi tare da su. "Ana zarginsu ne da laifin sama da fadi da kudaden al'umma. Kuma da zarar an gama binciken za'a gurfanar da su gaban kotu", a cewar Femi Babafemi

Martani

Sai dai Daraktan yada labarai na gwamnan jihar Kano, malam Sule Ya'u Sule ya ce wannan zargi sharri ne na abokan siyasa kuma gaskiya za ta yi halinta.

Yace ai haka ta taba faruwa ga gwamna mai ci Malam Ibrahim Shekarau, amma daga baya gaskiya tayi halinta.

"Shekara nawa yana kwamishina, amma ba wanda ya tunkare shi, sai yanyu da ya fito takara, wannan siyasa ce kawai", in ji Sule Ya'u Sule Alhaji Abdulkarim Daiyabu, shi ne shugban Rundunar Adalci a Najeriya, wanda shi ya kai korafin game da yadda aka batar da kudin kananan hukumomin gaban hukumar ta EFCC.

Ya kuma musanta cewa korafin na su nada alaka da siyasa.

A wata hira da BBC ta wayar tarho, yace majalisar dokokin jihar ce ta gudanar da bincike inda ta same su da laifi, amma aka yi watsi da lamarin.

Abinda yace shi ne dalilin su na kai maganar gaban hukumar ta EFCC.

Wakilin BBC Maude Rabi'u Gwadabe a Abuja, yace a yanzu haka dai al'ummar jihar Kano sun zubawa EFCC ido don ganin yadda wannan bincike zai kaya.