A yau za'a fara gasar cin kofin kwallon kafa

Gasar cin kofiin kwallon kafa na duniya a Afirka ta Kudu
Image caption Gasar cin kofiin kwallon kafa na duniya a Afirka ta Kudu

Nan da wasu saoi kalilan ne ake sa ran za a bude gasar cin kofin duniya, wanda za a yi a karon farko a nahiyar Afirka a Afirka ta Kudu.

Kasar Afirka ta Kudu mai masaukin baki za ta kara da kasar Mexico. Kasashe talatin da biyu ne za su fafata na tsawon wata guda, domin neman samun nasarar cin kofin duniya.

Ana sa ran tsohon shugaban Afirka ta Kudun Mista Nelson Mandela, zai bayyana a bukin bude gasar.

A jajiberin gasar Shugaban kasar Jacob Zuma ya shaidawa mutane cewa kasar na matukar farin cikin daukar nauyin gasar cin kofin duniyar na FIFA a shekarar 2010.

Shugaban yace 'Muna godiya ga FIFA a bisa daukar wannan mataki na kawo gasar cin kofin duniya a karon farko zuwa nahiyar Afirka'.