Kyrgyzstan ta kaddamar da dokar ta baci

Kyrgyzstan ta sanya diokar ta baci
Image caption Jami'an tsaro suna aikin samar da zaman lafiya a Kyrgyzstan

Mahukunta a kasar Kyrgyzstan sun kaddamar da dokar ta baci sannan suka sanya dokar hana yawo a birni na biyu mafi girma a kasar wato Osh da sauran garuruwan dake makwabtaka, bayanda aka samu barkewar rikici wanda yayi sanadiyyar rasuwar mutane a kalla goma sha biyu tare da jikkata wasu fiye da dari.

Rahotannin dake fitowa daga inda lamarin ya auku dai na nuna cewa, rikicin ya fara ne tsakanin gungun mutane masu gaba da juna a Vienman, daga bisani daruruwan matasa suka yi tururuwa zuwa cibiyar birnin, inda suka rika kwasar ganima a shagunan mutane tare da farfasa tagogin shagunan.

Wadanda suka shaida yadda lamarin ya auku dai sunce anyi ta jin karar bindigu tun cikin dare har zuwa wayewar garin yau. Haka kuma anga motocin sulke suna shawagi a cikin garin

Hukumomin kasar dai sun sanya dokar hana zirga zirga

Kasar Kyrgyzstan dai ta samu kanta cikin tashin hankali tun lokacin da aka kifar da gwamnatin kasar kuma tun daga wancan lokacinne gwamantin take ta kokarin kawo zaman lafiya