An fara muhawara kan sauyin yanayi a Nijar

Matsalar sauyin yanayi
Image caption Ana alakanta karancin abinci a kasashen Afrika da Matsalar sauyin yanayi

A jamhuriyar Nijar yanzu haka ana can ana wata muhawara kan samo hanyoyin da za su taimaka wajen tunkarar matsalolin sauyin yanayi a kasashe irin su Nijar da Nijeriya da Ghana.

Manufar taron ita ce tsara irin matsayin da kasashen Afrika masu fama da matsalar fari za su gabatar,a babban taron kasashen duniya da za a gudanar a Brazil ciki watan Agusta.

Wata kungiyar 'yan jarida ce dai ta shirya taron, wanda ake gudanarwa a Yamai babban birnin kasar.

A daidai loakcin da ake gudanar da wannan taro, hukumomi a kasar sun ce sun dukufa wajen neman hanyoyin magance matsalar karancin abincin dake addabar kasar a lokaci zuwa lokaci.

Sun ce sun gano cewa rashin inganta noman iri na daya daga cikin tushen wannan hali na yunwa da fatara da manoman ke yawan fadawa ciki.

A kokarin tunkarar matsalolin ne a ranar Laraba gwamnatin jihar Maradi ta kira wasu manya manyan manoman jihar, domin ba su shawarwari kan yadda za su bunkasa sana'ar ta noma .

An yi wannan taron ne karkashin jagorancin gwamnan jahar Kanal Garba Maikido, wanda ya bayyana muhimmancin kafa kungiyoyin manoma, domin samun taimako daga gwamnati.