Adadin man daya tsiyaye na BP ya ribanya

Tsiyayar mai a gabar tekun Mexico
Image caption Man daya tsiyaye a gabar tekun Mexico ya kai ganga dubu arba'in a rana

Kididdiga ta baya bayan nan a hukumance na nuna cewa man daya tsiyaya a tekun Mexico ya kai ganga dubu arba'in a rana, wanda ya ribanya kididdigar da aka yi a baya har sau biyu.

Kididdigar ta fito ne daga hukumar Safiyo da nazarin ma'aidinai wanda gwamnatin Amurka ta dauki nauyi, inda ta nuna cewa adadin man dake kwarara kafin kamfanin BP, wanda ya haddasa lamarin, ya kaiga toshe inda ya fashe da wata naura a cikin makonnin da suka gabata.

Sabbin alkaluman dai na nuni yadda al'amaura suka sake rinchabewa BP. Dangantaka tsakanin kamfanin BP da kuma gwmantin Obama dai yanzu ta kara tsauri fiye da ada.

An dai nemi shugaban kamfanin daya gabatar da kansa a fadar white house a mako mai zuwa a yayinda Shugaba Obama ya fito fili yana mai cewar dole ne kamfanin BP ya dauki nauyin gyara abubuwa, dole ne kuma ya biya ta'alin da wannan malalewar man ta janyo ga jahohi hudu dake da makwabtaka da inda lamarin ya uku.

Shugaban zai kai ziyara zuwa yankin a ranar litinin kuma wannan ita ce ziyarasa ta hudu zuwa gabar tekun tun lokacin da wata rijiya ta fashe a watan afrilu