An yanke hukunci a kan kisan kare dangi a Bosnia

Mutanen da aka yi wa kisan gilla
Image caption Mutanen da aka yi wa kisan gilla sun kai 8,000

Alkalai a kotun hukunta laifukan yaki a birnin Hague sun samu wasu Serbiyawan Bosniya biyu da aikata kisan kare dangi a 1995 a Srebrenica.

An yanke hukuncin daurin rai da rai, a kan hafsoshin sojin biyu, Vujadin, Popovic da Ljubisa Beara.

Akwai wasu Sabiyawan Bosniyar biyar da aka yanke ma hukuncin dauri kama daga shekaru biyar zuwa talatin, bayan samunsu da hannu a kisan kare dangin.