An nemi a kai Tandja Mamadou jinya a kasar waje

Tandja Mamadou
Image caption An yana fama da matsalar ido

A jamhuriyar Nijar hadin gwiwar kungiyoyin kare hakkin dan Adam CODDH, ya ce zai gabatar ma shugaban mulkin sojan kasar Janar Salu Jibo bukatar ya bayar da izini a kai tsohon shugaban kasar Tandja Mamadou kasashen waje domin a duba lafiyarsa.

Shugaban hadin gwiwar kungiyoyin na CODDH ne Malam Moustafa Kadi ya tabbatar da haka yau da safe yayin wani taron manema labarai a kan halin da tsohon shugaban kasar ke ciki.

Bayanai sun nuna tsohon shugaban kasar dai na fama da matsalar ido, da ciwon sukari, sannan kuma ba ya ji sosai, saboda haka akwai bukatar a duba lafiyarsa.

A jiya ne dai kungiyoyin kare hakkin dan adam din suka ziyarci tsohon shugaban kasar, da ministansa na tsaro, Malam Albade Abouba.