Ana tura wani sako mai tayar da hankali a jihar Kadunan Nijeriya

Taswirar Nijeriya
Image caption Taswirar Nijeriya

A jihar Kaduna wani sako ne na kar ta kwana wato text message yana neman tayar da tada hankulan jama'a a jihar.

Sakon dai wanda wasu wadanda ba a san ko su wanene ba suke aikawa, yana kira ne a bisa abinda sakon ya ce, tashi tsaye domin kalubalantar wani yunkuri na sanya sabon mataimakin jahar Alhaji Muktar Ramalan Yero a matsayin dan takarar gwamna a zaben shekara 2011.

Wannan dai ba karamar magana ba ce ga yan kudancin jahar, wadanda ke ganin kiyayya ce ake nunawa Gwamnan jihar Patrick Yakowa, bayan Architect Namadi Sambo ya zama mataimakin shugaban kasar.

Tuni dai gwamnatin jahar ta bayyana sakon a matsayin wani kokari na tada hankula a jahar da ta sha fama da rikice rikicen kabilanci da addini a baya.