Shugaba Obama da David Cameron zasu gana

Shugaba Obama zai gana da David Cameron na Birtaniya
Image caption Shugabannin kasashen Amurka da Birtaniya zasu gana domin tattauna batun malalar mai a gabar tekun Mexico

Shugaba Obama da Firayim Ministan kasar Birtaniya David Cameron, za su fara wata ganawa kan man dake kwarara a tekun Mexico a yau.

Kamfanin Birtaniya wanda ya haddasa tsiyayar man wato BP, na fuskantar matsin lamba sosai daga gwamnatin Amurka, don ya toshe inda man yake tsiyayar, da kuma tabbatar da cewar ya tsabtace ruwan da ya gurbata tare kuma da biyan diyya ga duk wadanda al'amarin ya shafa.

Tuni dai Shugaba David Cameron na birtaniya ya gana tare da shugaban kamfanin man na BP, inda ya bayyaya takaicinsa da damuwarsa a game da man dake tsiyaya a tekun Mexico

Ana saran kowane lokaci daga yanzu babban jami'in kamfanin man na BP zai gabatar da kansa a fadar White House dake Amurka