Rikicin Kyrgyzstan

Tankokin yaki a Kyrgyzstan
Image caption Tankokin yaki a Kyrgyzstan

Gwamnatin rikon kwariya a Kyrgyzstan ta umarci jami'an tsaron kasar da su yi harbi da niyyar kashewa a wani yunkuri na dakatar da rikicin kabilancin da ake yi a kudancin kasar, inda akalla mutane 80 suka rasa rayikansu, wasu karin fiye da dubu daya kuma suka samu raunika.

Dubban 'yan kabilar Uzbek ne dai ke tserewa daga Osh, birni na biyu mafi girma a kasar, yayinda ake cigaba da fada tsakanin 'yan Kabilar Kyrgyz da na Uzbek din, wanda shi ne tashin hankali mafi muni tun bayan da aka hambarar da shugaba Kurmanbek Bakiyev a cikin watan Afrilu.

Tun farko dai, gwamnatin ta Kyrgyztan ta nemi Rasha da ta tura sojojinta don taimakawa wajen kawo karshen tashin hankalin, amma Rashar ta ce ba ta da wani shiri a yanzu na aike da sojojinta zuwa kasar.

Karin bayani