An sabunta: 12 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 15:55 GMT

Ingila da Amruka sun yi kunnen doki

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

A cigaba da gasar cin kofin kwallon kafar duniya wanda ake yi a kasar Afirka ta Kudu, Ingila ta fafata da kasar Amurka inda aka tashi kunnen doki kowa na da ci daya.

Tun farko kuma an kara tsakanin Nijeriya da Argentina inda aka tashi Argentina na da ci 1 Najeriya kuma na nema.

A wasan farko kuma da aka yi, Koriya ta Kudu ta lallasa Girka da ci biyu da nema.

Najeriya da Argentina

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Duka kasashen biyu dai sun sha da kyar ne akan hanyarsu ta zuwa Afrika ta Kudu.

Najeriyar dai ta halarci gasar ne ba tare da dan wasanta Mikel Obi ba, wanda yake taka leda a kulob din Chelsea, sakamakon raunin da yake fama da shi.

Yayinda a nata bangaren Argentina ta dogara kan zakaran dan kwallon duniya Lionel Messi da Diego Militto da kuma Carlos Tarvez.

Shi dai kociyan Argentina Diego Maradona, na fatan shiga sahun wadanda suka taba lashe gasar a matakin 'yan wasa sannan suka maimaita hakan suna masu horaswa.

Kasashen biyu dai suna cikin rukunin na B ne, wanda ya kunshi kasashen Girka da kuma Koriya ta Kudu, wadanda su ma suka kara a yau. An dai tashi ne Koriya ta Kudu na da ci biyu Girka na nema.

Wasannin baya

A wasanni uku na baya bayan nan da kasashen biyu suka kara a matakin manyan 'yan wasa dai, Najeriya ba ta samu nasara a kan Argentina ba. KAsashen biyu sun hadu a zangon farko na gasar cin kofin duniya na shekarun 1994 da kuma 2002, inda Argentina ta samu nasara da ci 2-1 da kuma 1-0 a jere. Kasashen biyu kuma sun yi kunnen doki a karawar da suka yi a gasar Confederation a shekarar 1995. Sun dai tashi ba ci 0-0.

Hakazalika, Argentina ta samu nasara a kan Najeriya a wasan karshe na gasar cin kofin duniya na 'yan kasa da shekara 20, da aka kara a shekarar 2005, da kuma gasar Olympics a shekarar 2008. Sai dai Najeriya ta samu nasara a kan Argentina a shekarar 1996, inda aka tashi 3-2 a wasan karshe.

Ingila da Amurka

Sau daya dai kasar Amurka ta taba samun nasara a kan kasar Ingila a gasar cin kofin duniya a haduwar da suka yi a shekarar 1950. Karo na biyu da Amurkan ta samu nasara a kan Ingila shi ne a shekarar 1993, inda aka tashi 2-0.

Ita kuwa Ingila, ta samu nasara a kan Amurka sau bakwai.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.