Babban hafsan dakarun Birtaniya zai rataye kakinsa

Sir Jock Stirrup
Image caption Babban hafsan dakarun Birtaniya, Sir Jock Stirrup: Wasu na sukar Sir Jock da rashin yin abin a-zo-a-gani

A wani mataki na sauya dabarunta a Afghanistan, Birtaniya ta cire Air Chief Marshal Sir Jock Stirrup daga kan mukaminsa.

Sakataren tsaron Birtaniyan, Liam Fox, ya ce Sir Jock zai sauka daga kan mukaminsa na babban hafsan dakarun kasar cikin watanni uku ko hudu masu zuwa.

Sakataren tsaron ya ce zai so ya ga mutane masu kwarewa sosai a kan mukaman da suka dace da zarar an kammala bitar manufofin tsaro na bana.

Sir Jock ne dai babban hafsan dakarun tsaro na Birtaniya tun shekarar 2006.

Wadansu dai na sukar Sir Jock, wanda kwararren matukin jirgin saman yaki ne, da rashin yin abin a-zo-a-gani wajen kare dakarun Birtaniya dake bakin daga a Iraki da Afghanistan.

Mai yiwuwa a maye gurbin Sir Jock da wani hafsan sojojin kasa—tsakanin hafsan hafsoshin kasar, wanda ya jagorancin rundunar kungiyar tsaro ta NATO a Afghanistan, Janar Sir David Richards, da mataimakin babban hafsan dakarun tsaro, Janar Sir Nicholas Houghton.