Ana cigaba da rikicin kabilanci a Kyrgyzstan

wani gida da aka kona a birnin Jalalabad
Image caption wani gida da aka kona a birnin Jalalabad

Har yanzu ana cigaba da rikicin kabilanci a kudancin kasar Kyrgyzstan inda aka kona shaguna da wuraren shan shayi a birnin Jalalabad.

To amma rahotanni sun ce an daina jin harbe-harben da aka fara a ranar jiya Lahadi.

A halin da ake ciki, manyan jami'ai daga Rasha, da yankin tsakiyar Asiya, da kuma sauran kasashen yankin, na tattaunawa a birnin Moscow, domin duba yiwuwar tura dakaru zuwa Kyrgystan din, don kawo karshen tashin hankalin, wanda kawo yanzu ya janyo hallakar mutane fiye da dari.