Rikicin kabilanci a Kyrgyzstan: Dubbai sun tattara a bakin kan iyakar Uzbekistan

wani gida da aka kona a birnin Jalalabad
Image caption wani gida da aka kona a birnin Jalalabad

Kungiyar agaji ta red Cross ta duniya ta ce akwai kimanin 'yan kabilar Uzbek dubu goma sha biyar dake neman gujewa rikicin Kyrgyztan ke bakin iyakar Uzbekistan, bakin iyakar da gwamnatin Uzbekistan din ke son rufewa.

Tuni dai an yi kiyasin cewar yan kabilar ta Uzbek dubu 80 a Uzbekistan, kuma mataimakin Pirayim Minista Abdullahi Aripov ya ce kasar ba za ta amince da karin wasu ba saboda ba za su iya tsugunnar da su ba.

Uzbekistan ta bukaci taimakon kasashen duniya, hukumar kula da yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya na shirin aikewa da wata tawagar gaggawa.

An bayar da rahoton cewar wasu manyan jami'an Rasha da sauran kasashe a yankin sun amince a kan jerin matakan kokarin dakatar da tashin hankalin kabilancin a Kyrgyzstan.

Yarjejeniyar ta samu ne a wajen wani taron gaggawa na kungiyar tsaro ta yankin wadda ta hada da kasar ta Kyrgyzstan.

Tura dakarun kiyaye zaman lafiya na daga cikin matakan da ake tattaunawa a kai.