Babu Shugaban da ya cancaci karbar kyautar yabo ta Mo Ibrahim a Afrika

Mo Ibrahim
Image caption Mo Ibrahim

kwamitin bada kyautar shugabanci mai inganci a nahiyar Afrika, a karkashin gidauniyar Mo Ibrahim, ya kasa samun mutumin da ya cancanci karbar kyautar ta tsabar kudi dalar Amurka miliyan biyar a shekaru biyu jere.

Ana mika kyautar ce ga tsoffin shugabannin da suka hau mulki ta hanyar demokradiyya, suka kuma yi mulki nagari, sannan suka sauka yayin da wa'adinsu ya cika.

Shugaban gidauniyar Mo Ibrahim ya ce, saboda rashin samun wanda ya cancanci kyautar, za su bullo da shirin tallafawa kwararru kan harkokin jagorancin al'umma a Afirka, domin ganin an sami shugabanni na gari a nan gaba.

To amma a yanzu tambayar da ake ita ce: ko hakan na nufin cewa a halin da ake ciki ba shugabanci na gari a nahiyar Afirka ne? Masu lura da al'amura dai na ganin cin hanci da rashawa na daya daga cikin manyan ababuwan da ke haddasa wannan al'amari.