Karancin abinci na sa jama'a bara a Nijar

Matsalar yunwa a Nijar
Image caption Hajja da wasu daga cikin jikokin ta na bara a garin Maradi

Hajja na daya daga cikin fiye da rabin 'yan Nijar din da ke fama da karancin abinci, saboda matsanancin farin da kasar ke fama da shi.

Kungiyar bada agaji ta Burtaniya Save the Children, tace kimanin yara 400,000 ne ke fuskantar karancin abinci mai gina jiki.

Bayan da amfanin gonar da Hajja ta shuka suka lallace, sai tayi balaguro daga kauyen su zuwa garin Maradi tare da wasu jikokinta.

Ina lura da yara takwas, hudu daga cikinsu na tare da ni anan Maradi, sauran manyan suna gida a garin Mai Jangero.

Wajibi ne na dawo birni domin bamu da abinci ko kadan.

Bayan watanni hudu ko biyar abinda muka shuka ya kare.

Abinda yasa ya zamo wajibi mu dinga sayen abinci tun wancan lokaci.

Hakan ya sanya ni na cire yaran daga makaranta.

Bamu da isasshen kudi domin sayen abinci, don haka ba zan iya daukar nauyin karatun su ba.

Tace dukkan mu anan daka gani bara muke yi.

Mun dade muna ganin bala'i makamancin wannan a baya.

Image caption Jamhuriyar Nijar ta dade tana fama da mummunan fari

Amma bana abin yafi kauri, saboda jama'a da dama basu yi noma ba.

Kuma duk lokacin da aka fuskanci matsala irin wannan, to wajibi ne mu koma barace-barace.

Idan yanayi yayi kyau mukan samu buhu 80 a kowacce kaka.

Amma bana buhu15 kawai muka iya nomawa.

Ba mu da zabi illa mu fito kan tituna domin yin bara ko ma samu kudi.

Muna tura abinda muka samu ga 'yan uwanmu da ke gida domin su samu na abinci.

Muna yin barar ne da yamma bayan kammala sallah.

A wasu lokutan mukan samu saifa 400 (kimanin kwabo 70 na dalar Amurka) a kowacce rana.

Mukan sayi abinda muke bukata mu ci, sannan mu aika ragowar gida.

Ban san ainahin lokacin da za mu koma kauyen mu ba.

Idan damuna ta tsaya, kuma na samu kudi, to zan koma gida.

Idan kuwa babu isasshen ruwa, to hakika za mu zauna a cikin gari mu ci gaba da bara.