An kaddamar da Hukumar zabe a Jumhuriyar Nijer

Taswirar Jumhuriyar Nijer
Image caption Taswirar Jumhuriyar Nijer

An kaddamar da hukumar zabe mai zaman kanta a Jumhuriyar Niger, watau CENI, a shirye-shiryen da ake yi na mayar da kasar bisa tafarkin demokradiyya, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

Mambobin CENIn sun hada da wakilan jam'iyun siyasa da na gwamnati da kungiyoyin kwadago da na farar hula.

A jawabin da ya yi a lokacin bikin kaddamarwar, Praminista Mahamadou Dandah ya bada tabbacin cewa hukuma ce mai cikakken iko, wadda ba zaa yiwa shishigi ba.

A ranar 1 ga watan Maris na badi ne sojoji masu mulki suka yi alkawarin rantsar da zababben shugaba a Niger din.