Malaman kwalejojin ilimin Najeriya za su yi yaji

Taswirar Najeriya
Image caption Harkar karatun dubban dalibai a Najeriya za ta tsaya sakamakon yajin da malaman kwalejojin ilimi za su shiga

A Najeriya, yau ne malaman manyan kwalejojin horon malamai dake fadin kasar za su shiga wani yajin aikin gargadi na mako guda.

Hakan dai ya biyo bayan gazawar gwamnatin tarayyar kasar ne na cikawa malaman alkawuran da ta daukar musu a watan Fabrairun bana na kara masu albashi da kuma wadansu kudaden alawus-alawus.

Kungiyar malaman ta ce idan bayan nan gwamnatin ba ta biya masu bukatunsu ba, to za su shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani daga ranar Litinin, 28 ga wannan watan na Yuni.

Hakan dai zai iya kawo tsaiko a harkar karanatar da dubban daliban da ke karatu a wadannan kwalejoji a fadi kasar.

Sai dai gwamnatin Najeriyar ta bukaci malaman da su jinkirta zuwa karfe goma sha biyun rana, lokacin da ta ce kafin sannan za su ga sako a asusunsu na ajiyar banki.

To amma kungiyar malaman ta ce babu abin da zai hana yajin aikin; sai dai in sun ga karin, za su sake zama don tattaunawa a kan matakin da ya kamata su dauka.