Rahoto kan kisan Bloody Sunday ya fito!

Daya daga cikin wadanda sojojin suka harba.
Image caption Sojojin Birtaniya sun fuskanci suka cewar sun bude wuta kan mutanen da ba sa dauke da makamai.

Binciken da aka gudanar kan kashe-kashen Bloody Sunday - ko Lahadin da aka zubar da jini - a yankin Ireland ta arewa a 1972, ya nuna cewa, sojan Birtaniya ba su da hujjar harbin fararen hula.

Rahoton ya ce dukkan wadanda aka kashe a lokacin zanga zangar neman 'yanci, su goma sha ukku, ba su yi wata barazana ba.

Praministan Birtaniya, David Cameron, ya nemi gafara a madadin gwamnatinsa, da kuma kasar baki daya.

Tsohon babban hafsan dakarun Birtaniya, wanda ya fara aikinsa a lardin Ireland ta arewa, Janar Sir Richard Dannatt ya ce, duk da yake abin da sojin suka aikata, abin suka ne, amma hakan ba yana nuna dabi'ar sojojin Birtaniya ba ne.

Iyalan wadanda kashe kashen suka shafa, sun bayyana gamsuwa da sakamakon rahoton.