Majalisun dokokin jihohin Najeriya sun karbi tsarin mulkin da aka yi gyara

Majalisar dokoki ta kasa a Najeriya
Image caption Majalisar dokoki ta kasa a Najeriya

Majalisar dokoki na kasa a Najeriya ta mika kundin tsarin mulkin da ta yi wa gyara ga shugabannin majalisun dokokin jihohi domin amincewarsu.

Kodayake an yi gyara ga sauran sassan kundin tsarin mulkin Nigeria, amma gyaran ya fi maida hankali ne ga harkokin zabe.

Sassa arbain da daya ne majalisar dokokin tarayya ta amince da yiwa gyara.

Akwai dai bukatar samun kashi 2 bisa ukku na majalisun jihohi su amince da shi tukuna kafin ya zamanto doka, wato sai jihohi 24 daga cikin 36 sun amince tukunna.