Najeriya za ta rage dogaro da man fetur

Taswirar Najeriya
Image caption Ministan kudi na Najeriya ya ce kasar za ta bunkasa harkar samar da wutar lantarki da noma

Ministan kudi na Najeriya ya shaidawa BBC cewa kasar na bukatar rage dogaron da tattalin arzikinta ya yi da man fetur.

A hirarsa ta farko da wata kafar yada labarai ta talabijin ko rediyo, ministan, Dokta Olusegun Aganga, ya tattauna ne a shirin harkokin kasuwanci na gidan talabijin na BBC a kan illolin da man fetur din ya haifarwa kasar.

A yankin Niger Delta, inda bututan man suka ratsa ta yankunan da ke fama da talauci, ana fama da tashe-tashen hankula.

Sannan kuma sauran bangarorin tattalin arzikin kasar, musamman harkar noma, ba sa bunkasa yadda ya kamata saboda an fi karkatar da hankali da ma kudade ga bangaren man fetur.

Najeriyar ce dai ta goma a jerin kasashen da ke samar da danyen man fetur a duniya, kuma man ne ke sama mata kusan dukkan kudin shigarta, da ma akasarin kudaden da gwamnatocin kasar ke kashewa.

To amma duk da dimbin man fetur din da kasar ke da shi, tana fama da yawan dauke wutar lantarki, hatta a ma'aikatar kudi da sauran ma'aikatun gwamnati.

Ministan da ke kula da ma'aikatar ta kudi ya yiwa BBC karin bayani a kan illolin da man fetur ya haifar: “Da fari man fetur ya kawo babbar fa'ida ga Najeriya.

“To amma sannu a hankali sai al'amura suka sauya, man ya zama tamkar wani bala’i.

“A wannan lokacin ne kuma ya kamata a fara tunanin irin matakin da ya kamata a dauka, a kuma fara tunanin yadda za a tabbatar da cewa an rage dogaro a kan mai don samun kudin shiga”.

Sai dai sauyin da ministan ke magana a kai ba abu ne mai sauki ba.

Dokta Aganga ya ce yana kokarin sake fasalin harkar samar da wutar lantarki a kasar, da kuma jawo hankalin masu zuba jari daga waje don su zuba jari a bangaren noma da kiwo.

To amma wannan ba abu ne da zai faru dare daya ba.