Illolin hakar mai ga muhalli a Najeriya

Illolin malalar mai a Najeriya
Image caption Hakar man fetur ta dade tana haifar da illa ga mazauna yankin Naija-Delta

A yanzu dai an shafe fiye da shekaru hamsin da biyu ke nan ana hakar danyen man fetur a yankin Neja-Delta da ke kudancin Najeriya.

Yankin Neja-Deltan ya dade yana jan hankalin kungiyoyin kare hakkin dan adam da masu fafutukar kare muhalli da masu neman adalci kan harkokin kasuwanci a duniya.

Korafin na su dai ya dogare ne kan yadda kamfanonin hakar mai a yankin suke gudanar da ayyukan su.

Ana dai zargin manyan kamfanoni da suka hada da Shell da Chevron da Mobil da laifin cutar jama'ar yankin ta hanyar lalata musu muhalli sakamakon ayyukan hakar man.

Irin wadannan illoli wadanda suke a zahiri a ko'ina cikin yankin, suna hana jama'a gudanar da ayyukan noma da kamun kifi.

A wasu lokutan ma sukan hana mutane samun isasshen ruwan sha.

Ana dai alakanta hakan da shekarun da kasar ta shafe cikin mulkin kama karya na soji da kuma zargin cin hanci da rashawa da ake yiwa mafiya yawan jami'an gwamnati a kasar.

Wadanda ake zargin cewa suna amfana daga cinikayyar man ba bisa ka'ida ba, tare da barin jama'ar yankin cikin matsanancin talauci.

Wannan lamari na kara jan hankalin jama'a a daidai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce kan malalar da mai ke yi a kogin Mexico na Amurka.

Shekaru goma kan tafarkin dimokradiyya

Yau shekaru goma kenan tun bayan da kasar ta koma kan tafarkin dimokradiyya, amma har yanzu mazauna yankin na Naija-Delta na cikin talauci da kuncin rayuwa. Najeriyar ce dai ta goma a jerin kasashen da ke samar da danyen man fetur a duniya, kuma man ne ke sama mata kusan dukkan kudin shigarta, da ma akasarin kudaden da gwamnatocin kasar ke kashewa.

To amma duk da dimbin man fetur din da kasar ke da shi, tana fama da yawan dauke wutar lantarki, hatta a ma'aikatar kudi da sauran ma'aikatun gwamnati.

Sai dai wasu na da ra'ayin cewar aikin hakar man na kawo koma baya ta fuskar muhalli ga jama'ar yankin na Niger-Delta, ganin irin halin da yankin ke ciki.

Image caption Yankin Naija-Delta nada arzikin mai sosai, amma jama'ar na fama da talauci

Daina dogaro kan man fetur

A wani bangere na rahotanni na musamman da BBC ke gabatarwa kan illar hakar mai ga jama'a da muhalli, sashin kasuwanci na BBC ya tattauna da ministan kudi na Najeriya Dokta Olesegun Aganga.

Wanda ya bayyana cewa kasar na shirin sauya tunani kan hanyoyin samun kudaden shigarta.

Ministan ya yiwa BBC karin bayani a kan illolin da man fetur ya haifar: "Da fari man fetur ya kawo babbar fa'ida ga Najeriya.

"To amma sannu a hankali sai al'amura suka sauya, man ya zama tamkar wani bala'i.

"A wannan lokacin ne kuma ya kamata a fara tunanin irin matakin da ya kamata a dauka, a kuma fara tunanin yadda za a tabbatar da cewa an rage dogaro a kan mai don samun kudin shiga".

Sai dai sauyin da ministan ke magana a kai ba abu ne mai sauki ba.

"Ba zai faru dare daya ba"

Dokta Aganga ya ce yana kokarin sake fasalin harkar samar da wutar lantarki a kasar, da kuma jawo hankalin masu zuba jari daga waje don su zuba jari a bangaren noma da kiwo.

A cewarsa wannan ba abu ne da zai faru dare daya ba.

Najeriya dai ta dogara ne sosai a kan cinikin man don samun kudaden shigarta.

Malalar mai a kogin Mexico

Matsalar man da ake fuskanta a kogin na Mexico dai na ci gaba da jan hankulan jama'a da dama a duniya.

A bayyane take dai cewa, wannan al'amari ne da bai cika aukuwa ba: kamfanin mai na BP, wanda ke tsakiyar takaddamar, ya ce ya hako mai a wasu rijiyoyin mai guda 1,500 wadanda ke tekun Mexico ba tare da fuskantar wata matsala ba.

Sai dai mutane da dama za su ce hakan ba wata hujja ba ce idan aka yi la'akari da cewa, lamarin da ya auku ya janyo wani gagarumin bala'i fiye da yadda ake tunani.

Shugaba Obama ya bayyana lamarin da cewa wani bala'ine da yayi kama da hare-haren sha daya ga watan Satumba.

Kasashe masu tasowa da dama dai na fuskantar barazana daga illolin hakar mai ko akan kasa ko kuma a cikin teku.

Musamman ganin yadda kasashe irin su Amurka, wadanda su ka ci gaba ta fuskar kimiyya da tattalin arziki, amma sun kasa shawo kan matsalar.

Idan har ana so a kare jama'a daga illolin masu dangantaka da wannan, to wajibi a tashi tsaye, sannan a fifita lafiyar jama'a da muhallin su kan kudi ko dukiya.