Kasashen Korea sun je gaban kwamitin sulhu

Cheonan, jirgin ruwan Korea ta Kudu da ya nutse
Image caption Cheonan, jirgin ruwan Korea ta Kudu da ake zargin Korea ta Arewa da nutsar da shi a watan Maris

Kasashen Korea ta Arewa da Korea ta Kudu sun bayar da bahasi a Majalisar Dinkin Duniya dangane da takaddamar da ke tsakaninsu kan nutsewar wani jirgin ruwan yaki na Korea ta Kudu.

Jakadun kasashen biyu dai sun gana a lokuta daban-daban da mambobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar.

A makon da ya gabata, Korea ta Kudu ta bukaci kwamitin sulhun ya dauki matakin ladabtarwa a kan Korea ta Arewa saboda harin da ake zargin Korea ta Arewan ta kai a kan jirgin ruwanta a watan Maris, wanda ya hallaka mutane arba'in da shida.

Tawagar Korea ta Kudu ce dai ta fara shiga dakin taron, inda ta gabatar da cikakkun hujjojin da ta ce sun tabbatar da cewa Korea ta Arewa ce ta nutsar da jirgin ruwan.

Tawagar ta kuma kafa hujjoji da hotunan bidiyon da ke bayani a kan sakamakon binciken kasa-da-kasa da aka gudanar a kan lamarin.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar masu binciken, Yoon Dukyong, ya ce sun samu kyakkyawar tarba a wajen kwamitin sulhun.

“Muna fatan da wadannan hujjojin, kwamitin sulhu zai dauki matakin da ya dace, kuma a lokacin da ya dace don ladabtar da Korea ta Arewa”, inji Mista Yoon.

Daga bisani, tawagar Korea ta Arewa ta shiga dakin taron, inda a cewar jami'an diflomasiyyar Majalisar Dinkin Duniya, ta nemi a ba jami'anta dama su ziyarci inda al'amarin ya auku.

Tawagar ta kuma yi watsi da hujjojin Korea ta Kudun da cewa na bogi ne.

Mataimakin jakadan Korea ta Arewa a Majalisar Dinkin Duniya, Pak Tok Hun, ya ce: “Mu aka yiwa laifi.

“Za mu so mu fayyace matsayinmu a nan; za mu kuma yi bayanin matsayinmu dangane da wannan al’amari”.

Har yanzu dai ba a yi ittifaki a kan matakin da ya kamata a dauka ba: yayinda wasu mambobin kwamitin sulhun ke cewa sun gamsu da hujjojin Korea ta Kudu, wasu kuma sun ki su ce uffan.

Musamman, Rasha da China—wadda ita ce babbar kawar Korea ta Arewa—sun ki yanke hukunci a kan binciken har yanzu.

Sai dai ko kasashen da ke goyon bayan Korea ta Kudu ma sun ce wajibi ne duk wani mataki da kwamitin sulhun zai dauka ya kaucewa rura wutar rikici a yankin na Korea.