Hukumomin tsaron Ghana na bincikar tsoffin mayakan Niger Delta

Jami'an cibiyar binciken manyan laifufuka a kasar Ghana, watau BNI, sun yi wa shugaban kungiyar 'yan Niger Delta dake Ghana, Francis Okporokpo tambayoyi, kan ikirarin da yayi cewa tsoffin masu fafutukar na Najeriya su kimanin dubu 3, sun shiga cikin kasar ta Ghana.

A cewar Mr. Francis Okporokpo, bayan da suka ajiye makamai, abinda suke so shi ne, samun hadin kan ofishin jakadancin Najeriya dake Ghana, domin kiran wani babban taron tattaunawar zaman lafiya tsakaninsu da gwamnatin Najeriya.

Tsoffin masu fafutukar na kukan cewa, gwamnatin Najeriya bata cika alkawurran da tayi masu ba bayan sun ajiye makamansu.