Zanga zangar adawa da gina jami'a a Sokoto

Zanga zanga a Madorawa
Image caption Zanga zanga a Madorawa

A Najeriya, mazauna kauyen Madorawa dake wajen birnin Sakkwato, sun yi zanga zanga a yau, domin nuna rashin amincewa da shirin gwamnatin jahar na sake wa mazauna yankin matsugunni, domin kafa wata jami'a mallakar jihar a wurin.

Masu zanga zangar, wadanda yawancinsu manoma ne, sun ce kafa jami'ar a wurin zai raba su da gonakinsu masu albarkar kasar noma, tare kuma da tarwatsa al'ummar da ta shafe sama da shekaru dari zaune wuri daya.

Gwamnatin jahar Sakkwaton dai ta ce ta yanke shawarar kafa jami'ar ce da amincewar wasu shugabannin al'ummomin, kuma ba gudu ba ja da baya.