Musulmai a Jos sun kai karar 'yansanda

Taswirar Najeriya
Image caption Najeriya ta dade tana fama da rikicin addini dana kabilanci

Shugabannin musulmai sun bukaci rundunar 'yansandan kasar ta biya su diyyar Naira miliyan dubu dari sakamakon kakashe `yan uwansu da aka yi a fadan kabilanci, dana addini da ya faru a jihar ta Pilato.

Wadanda suka shigar da karar dai na tuhumar tsohon kwamishinan `yan sanda na jihar Pilaton ne da furta kalaman da suka haddasa rikicin, yayin da ita kuma hukumar gidan talabijin da rediyo ta jihar Pilato suke zarginta da iza wutar rikicin, ta hanyar yayata kalaman tsohon kwamishinan.

Sai dai rundunar `yan sanda ta Najeriyar ta ce a shirye ta ke ta kare kanta daga wannan zargi a gaban kotu. Kuma Kotun ta ware ranar 19 ga watan gobe don fara sauraron karar.

Jihar Pilato dai ta sha fama da fadade-fadacen da ke da nasaba da addini,da kuma kabilanci,abinda ya yi sanadiyar halakar jama'a da dama.