Najeriya ta tallafawa Nijar da Chadi

Shugaban Najeriya Gooluck Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya Gooluck Jonathan

Shugaban Najeriya Dakta Goodluck Jonathan ya umarci ma'aikatar aikin gona ta kasar ta aika da ton dubu goma sha biyar na hatsi ga kasashen Nijar,da Chadi domin rage tsananin yunwar data addabi wasu al'ummomi a kasashen.

Wata majiya a ma'aikatar aikin gona ta Najeriya ta tabbatarwa da BBC cewa shugaban kasa Dakta Goodluck Jonathan ya bayyana rashin jin dadinsa da irin halin yunwar da kasashen Nijar da kuma Chadi suka shiga.

Kazalika kamfanin dillacin labaran Najeriya ya ambato karamin ministan ma'aikatar aikin gonar Alhaji Nojeem Awodele, na tabbatar da umarnin na Shugaba Jonathan.

Ministan ya ce Najeriya za ta aike da hatsin ne don yin biyayya ga karin maganar nan da ke cewa abin da ya taba hanci ba ya barin idanu.

Ya kara da cewa rashin aikawa da tallafin abincin ka iya yin barazana ga makotan kasashen na Nijar da kuma Chadi.

Kasashen Nijar da Chadi dai na fama da matsalar yunwa sakamakon karancin abinci da suke fuskanta abinda ya sa suke ketarawa makotan kasashe don samun abincin.