Malalar mai cin fuska ce ga Amurkawa: In ji Obama

Kogin Mexico
Image caption Har yanzu mai na ci gaba da kwarara a kogin Mexico

Shugaban Amurka Barrack Obama ya bayyana matsalar malalan man daya abku a tekun Mexico da cewa wani cin fuska ne ga daukacin Amrukawa, kana kuma wata Ishira ce dake nuna gazawar ci gaban kimiyya.

A wani jawabi daya gabatar ta gidan talbijin ga jama'ar kasar, shugaban ya zargi kamfanin mai na BP da ganganci.

Inda ya ce ba zai gaza ba har sai ya ga cewa kamfanin ya biya tarar matsalar da malalar man ta haddasa.

Shugaba Obama ya jaddada cewa, zamu yaki wannan matsalar ta malalar mai ta kowacce hanya, za kuma mu sa kamfanin mai na BP da ya biya tarar duk matsalolin da malalar man ta haddasa.

kana kuma zamu yi iyakacin kokarinmu na ganin mun taimakawa al'umomin dake gabar teku domin su farfado daga wannan matsalar.

A yayin da shugaban ya ke magana a ofishinsa, ya nuna muhimmancin da wannan lamarin ke da shi.

Biyan diyya

Shugaba Barak Obama ya bayyana aniyarsa ta yin maganin matsalar da ake gani a matsayin wata babbar masifar da ta shafi muhalli, wacce kasar Amurka ke fuskanta a tsawon tarihinta.

Ya shaidawa kamfanin man BPn cewa dole ne ya biya duk barnar da malalar man ta jawo, sannan shugaban ya sha alwashin dawo da martabar tekun na Mexico.

Kazalika ya ce gwamnatinsa za ta samar da wata na'ura da za ta rika lura da al'amuran da suka danganci hakar mai.

Sannan ya ce zai yi garanbawaul ga hukumar da ke lura da kamfanonin man kasar.

Shugaba Obama bai tsaya nan ba, ya yi magana kan yadda ya kamata kasar ta rungumi batun amfani da makamashi, kana ta daina amfani da mai .

Sai dai abinda Amurkawa suka fi bukatar gani a yanzu, shi ne a tsayar da malalar man daga tekun na Mexico.