Okogie yace Nijeriya na cikin mawuyacin hali

Tutar Nijeriya
Image caption Tutar Nijeriya

Wani shugaban mabiya darikar katolika a Nijeriya, Cardinal Olubunmi Okogie ya ce Nijeriya ta na cikin wani hali na tsaka mai wuya, da ke bukatar shugabanni su kauce wa kokarin gina kansu maimakon kasa.

Cardinal Okogie ya bayyana haka ne a lokacin bikin cikarsa shekaru 74 da haihuwa.

Ya ce akwai bukatar a yi la'akari da wannan kira nasa, yayinda zaben shekara ta 2011 ke kara kawo jiki.

Ya kuma yi kira ga jama'a da su koma ga Allah, su kuma guji aikata alfasha.