Mace mai tukin tirela a Najeriya

Hajiya Rabi'atu Abubakar
Image caption Hajiya Rabi'atu na da yara biyu.

Sana'ar tukin achaba,tasi ko manyan motoci wata sana'a ce da aka fi sanin cewar maza ne ke gudanar da ita musamman a arewacin Najeriya domin tafiyar da rayuwar su ta yau da kullum a bisa dalilan da ake ganin cewar matan ba kasafai sukan jure wahalhalu da hadarurruka da suka danganci tuki bisa manyan titunan kasar ba.

To sai dai wakiliyar BBC dake Maiduguri ta ci karo da wata mata dake sana'ar tuka Tirelar siminti a tsakanin jihohin kudanci da arewacin Najeriya lokacin da tayi lodi zuwa Maiduguri.

A bayan tashar jiragen kasa dake Unguwar Abbaganaram cikin garin Maidguri wata karamar tashar manyan motocin tirela da kan sauke ko kuma yi lodin kayayyaki ya zuwa wasu sassan jihohin kasar,a nan ne kuma ta iske wannan mata mai matsakaicin shekaru Hajiya Rabi'atu Abubakar inda ake sauke lodin kayan dake cikin tirelar da ta tuko daga kudu.

Image caption Hajiya Rabi'atu na lodin siminti daga kudanci zuwa arewacin Najeriya

Hajiya Rabi'atu dai yar asalin jihar Katsina kuma wakiliyar BBC ta fara da tambayar ta yadda ta fara wannan sana'a ta tukin mota a hirar da suka yi.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti