Isra'ila za ta sassauta killace Gaza

Image caption Isra'ila ta hana shiga da kayayyakin gini yankin Gaza

Isra'ila ta bada sanarwar cewar za ta sassauta killace zirin Gaza da ta yi domin barin fararen hula da kayayyaki su samu shiga yankin Falasdinawa.

Wannan matakin da kasar ta dauka ya biyo bayan matsin lambar da take fuskanta game da killace Gazan da ta yi.

Kasashen duniya sun soki Sojojin Isra'ila game da harin da suka kaiwa jiragen ruwan da za su kai agaji Gaza a watan daya gabata.

Isra'ila da Masar sun killace Gaza ne bayan Kungiyar Hamas ta karbi mulki a yankin a shekarar dubu biyu da bakwai.

Majalisar zartarwar Isra'ila ta dauki wannan matakin sassauta killacewar ne bayan wata tattaunawa da tayi na tsawon kwanaki biyu.

Duk da cewa dai Isra'ila ta ce za ta sassauta killacewar, sai dai ta ce Sojojin ruwanta za su ci gaba ta sintiri domin hana shigowa yankin ta ruwa.

Isra'ila dai ta ce za ta bari a shigo da kayayyaki cikin Gaza, kamarsu kayan abinci da kayan kicin da kayan amfanin Ofis da kuma na wasan yara.

Isra'ilan ta ce ba za ta bari a shigo da kayayyakin gini ba kai tsaye, a yayinda ta ce sai jami'an kasa da kasa sun sa ido domin lura da irin ayyukan da za a yi da su.

Isra'ila ta hana shiga da siminti da kuma karafa yankin Gaza, saboda tana zargin cewa kungiyar Hamas za ta yi amfani da su wajen ginin makamai da shinge.

A watan daya gabata ne dai wasu masu fafutukar kwato hakkin Gaza su kayi yunkurin shiga yankin ta ruwa, abin da kuma Isra'ila ta hana, wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane tara.