An tsare tsohon ministan ma'adanai a Nijer

Shugaban Nijar Salou Djibou
Image caption Shugaban Nijar Salou Djibou

Hukumar 'yan sanda a Nijar na ci gaba da tsare tsohon ministan ma'adinai da makamashi na kasar Mohamed Abdullahi, tare da wasu mutane uku, ciki har da dan tsohon shugaban kasa Tandja Mammadou.

Kamun nasu ya biyo bayan wani bincike ne da aka gudanar kan zargin aikata wasu abubuwa da suka saba ka'ida, a ma'aikatar, zamanin mulkin shugaba Tanja.

Lamarin dai yana da nasaba da wasu kwangiloli da aka rattaba hanu kan su da wasu kamfanoni na kasashen waje. Kamfanonin hakar ma'adinai na kasashen waje da suka hada da na Faransa da China na da dimbin jari a kasar ta Nijar.