Kasar Syria ta caccaki Isra'ila

Kasar Syria  ta yi suka ga Israela
Image caption Shugaban kasar Syria,Bashar al-Assad

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad ya ce kai harin da Israela ta yi kan jiragen da ke dauke da kayayyakin agaji zuwa yankin Gaza ya nuna rashin kaunar zaman lafiyar da Israelan ke da shi

A wata hira da ya yi da BBC, shugaban ya zargi gwamnatin Israela da nuna son kai, inda ya ce gwamnatin bata maida hankali ba na neman zaman lafiya fiye da kowacce gwamnatin kasar da aka taba yi.

Shugaba Assad ya musanta cewa yana aikawa kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon makamai.

Israela, da Amurka, da kuma Birtaniya sun nace cewa shugaba Assad na aikawa da manyan makamai ga kungiyar ta Hezbollah.