An samu baraka a jam'iyyar PDP a Kaduna

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Wasu 'yan jam'iyyar PDP da ke mulkin Najeriya sun yi zargin cewa ana dakatar da su daga jam'iyyar, a reshenta na jihar Kaduna saboda wasu dalilai na siyasa.

'Yan jam'iyyar sun yi kira ga gwamna Jihar, Mista Ibrahim Yakowa, ya sa baki a cikin batun don gudun kada rikicin ya yi sanadiyyar faduwar jam'iyyar a zabe mai zuwa.

Sai dai shugabannin Jam'iyyar sun musanta korafe-korafen, inda suka ce komai na tafiya daidai a jam'iyyar.

Jam'iyyar PDP dai ta sha fama da rikice-rikicen cikin gida, abin da masu sharhi ke gani na barazana ga dorewarta.

A baya dai an alakanta irin wannan rikici da barakar da ke akwai tsakanin tsohon gwamnan jihar, kuma mataimakin shugaban kasa a yanzu, Namadi Sambo, da mutumin da ya gada Sanata Ahmed Makarfi.

Amma sai dai mutanen biyu sun yi sulhu bayan da uwar jam'iyyar ta kasa ta kafa wani kwamiti wanda ya shiga tsakanin su.